Chelsea ta Doke Manchester United 3-1

Chelsea United Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Chelsea tana matsayi na 3 a teburin Premier

Damar da Manchester United take nema na kare kanbun kofin Premier ya kubuce mata a lokacin da Samuel Eto'o ya zura kwallaye uku a karawar da Chelsea ta samu nasara a gasar Premier.

United karkashin jagorancin David Moyes ta fara wasan da kai hare - hare, kafin Eto'o ya fara zura kwallo a raga bayan da kwallo ta doki kafar Michael Carrick.

Eto'o ya kara kwallo ta biyu kafin aje hutu bayan da ya tsinci kwallo a bugun da Gary Cahill, sannan ya kara ta uku bayan an dawo daga hutu.

Javier Hernandez ya farkewa United kwallo daya kafin a baiwa mai tsaron baya Nemanja Vidic jan kati ya kuma futa daga wasan.

Rashin nasarar da United ta yi, yasa tazarar maki 14 tsakaninta da Arsenal wacce take matsayi na daya a Teburin Premier.