Ba Rooney da van Persie a karawar stamford Bridge

Moyes Mourinho
Image caption Chelsea za ta karbi bakuncin United a Stamford Bridge

'Yan wasan Manchester United Wayne Rooney da Robin Van Persie ba za su buga karawar da kungiyar za ta yi da Chelsea ba, sakamakon jinya.

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce dan wasan da ya dawo kungiyar Nemanja Matic da aka sayo kan kudi fan miliyan 21 ba zai buga karawa da United ba.

Frank Lampard ya samu saukin rauni na ciwon agara sai dai Branislav Ivanovic ba zai samu wasa ba sakamakon rauni da ya ji a gwiwa.

Mai tsaron baya na United Fabio zai kammala hutun wasanni uku bayan da ya karbi jan kati.