Za a fada da filin Barcelona Nou camp

Barcelona Nou Camp Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Filin da za a fadada domin diban 'yan kallo 105,000

Barcelona za ta ci gaba da wasanni a filinta na Nou Camp bayan da kungiyar ta sanar da shirin fadada filin da zai ci tsabar kudi fan miliyan 496 da zai dauki 'yan kallo 105,000.

A kuru'un da aka kada a taron da ta gudanar ranar Litinin, daraktocin kungiyar sunki amincewa da barin filin da yake daukar 'yan kallo 99,358 zuwa wani sabon wuri da za a tanada.

Filin zai ci gaba da karbar bakuncin wasanni a lokacin da ake gudanar da aiki da ake sa ran kammalawa a shekarar 2021.

Barcelona ta fara wasa a Nou Camp tun lokacin da aka yi bikin bude filin da aka gina a shekarar 1957, kuma filin ya karbi bakuncin wasan karshe na cin kofin zakarun Turai a shekarar 1989 da 1999, da bakuncin kofin duniya 1982 da wasan Olympics a shekarar 1992.

Barca ta yi rashin nasarar wasa daya kacal daga cikin wasanni 50 da ta buga a Nou Camp a baya bayan nan, ta lashe wasanni 46.