FIFA: Champagne na son ya gaji Blatter

Jerome Champagne
Image caption Champagne na fatan sauya alkiblar Fifa

Tsohon mataimakin sakatare janar na Fifa, Jerome Champagne ya kaddamar da aniyarsa na maye gurbin shugaban Fifa Sepp Blatter.

Dan Faransa da ya samu goyon bayan Pele, ya sanar da niyarsa na zamo wa Shugaban Fifa a dakin taron manema labarai a Landan ranar Litinin.

"Muna bukatar sabuwar Fifa, a yanayi na siyasa, wacce za a daraja ta, mai alkibla ta gari da za ta yi aiki tukuru", inji Champagne.

Za a gudanar da zaben Fifa a Zurich a watan Yuni a shekara ta 2015.

Champagne, mai shekaru 55 ya yi aiki kut da kut tare da Blatter daga shekarun 2002 zuwa 2005 kafin ya bar Fifa a shekarar 2010.

Tun daga lokacin ya koma jami'in tuntuba na kasa da kasa a shiyyoyin da ake tashin hankali da suka hada da Kosovo da Palestine da Israel da Cyprus.

Blatter, zai cika shekaru 78 a watan Maris, kuma yana shugabancin Fifa tun daga shekakar 1998. Dan Switzerland har yanzu bai bayyana aniyar ko zai tsaya takara a karo na biyar a jere ba.

Zakakurin dan kwallon Brazil Pele, wanda ya lashe kofin duniya karo uku ya ce yana marawa Champagne baya.