Seedorf ya yi murna da Milan ta bashi koci

Clarence Seedorf Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ya fara da lashe wasan farko a matsayin koci

Sabon kocin AC Milan Clarence Seedorf ya yabawa kungiyar da ta bugi kirji ta bashi aikin horadda klub din, bayan da ya karbi ragamar da kafar dama.

Duk da cewa Seeedorf mai shekaru 37 bai taba kocin kowacce kungiya ba, amma an bayyana shi da maye gurbin Massimiliano Allegri a makon da ya gabata.

Tsohon dan kwallon Milan mai wasan tsakiya ya jagorancu kungiyar da ta doke Verona da ci daya mai ban haushi ranar Lahadi a wasansa na farko a kocin kungiyar.

Clarence Seedorf shi ne dan kwallon da ya fara lashe kofin zakarun Turai karo uku a kungiyoyi daban-daban, ya dauka a Ajax a shekarun 1995 da Real Madrid a shekarar 1998 da kuma Milan a 2003 da 2007.

Milan za ta kara da Cagliari ranar Lahadi a Sardinia.