Zoopla ya yanke hulda da West Brom

Nicolas Anelka Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya nemi afuwa akan laifin da ya aikata

Kamfanin Zoopla da ke yiwa West Brom kayan wasanni ya yanke hulda da kungiyar, daga karshen kakar wasa ta bana sakamakon nunin da Nicolas Anelka ya yi da hannu da aka alakanta da jinjinawa 'yan Nazi.

Anelka ya yi nunin ne da hannayensa lokacin da ya zura kwallo a karawar da suka yi da West Ham ranar 28 ga watan Disambar 2013.

Hukumar FA ta Ingila na binciken lamarin domin sanin hukuncin da za ta dauka.

Tun daga lokacin West Brom ta ci gaba da amfani da dan wasan mai zura kwallo a raga, koda yake ya yi alkawarin ba zai sake kwatanta nunin da ya yi ba.

Yarjejeniya tsakanin kamfanin da kungiyar za ta kare a karshen kakar bana, sai dai Zoopla ya ce ba zai tsawaita sabuwar kwantaragi ba.