FA na tuhumar Nicolas Anelka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana kallon nuni kasan da Anelka ya yi da hannunsa a matsayin koyi da 'yan Nazi masu kin Yahudawa.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, ta tuhumi dan wasan West Brom Nicolas Anelka bisa nunin da yayi da hannunsa.

Anelka ya nuna kasa da hannunsa ne, a sigar da ake dauka koyi da 'yan Nazi masu kin Yahudawa ne, bayan da ya ci kwallo a wasansu da West Ham a gasar Premier ranar 28 ga Disamba.

Kamfanin Zoopla mai daukar nauyin West Brom zai kawo karshen alakarsa da kungiyar a karshen kakar bana saboda nunin na Anelka.

Dan wasan mai shekaru 34, wanda ya buga wasan da kungiyar ta yi kunnen doki da Everton, na da wa'adin karfe 6 na yammacin 23 ga Janairu ya mai da martani ga tuhumar.

West Brom dai za ta rasa dan wasan gaba mai zura kwallo idan aka dakatar da Anelka bayan da dan wasanta Shane Long ya koma Hull City.

Anelka ya sha alwashin ba zai sake yin nunin ba, wanda ya ce ya yi ne saboda goyon bayan mai ban dariyar nan na Faransa, Dieudonne M'bala M'bala wanda gwamnatin kasar ta haramta wa yin alamar a wasanninsa.