Morocco za ta kara da Nigeria a CHAN

Image caption 'Yan kwallon Afrika masu wasa a gida na fafatawa a kasar Afrika ta Kudu.

Morocco za ta kara da Nigeria a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar CHAN ta 'yan kwallon kafar kasashen Afrika dake wasa a gida.

Morocco da Zimbabwe sun shiga matakin daf da na kusa da na karshe a gasar ne bayan da suka fito daga rukunin B.

Uganda ce jagaba a ranar Litinin amma nasarar 3-1 da Morocco ta samu akanta ya bai wa Atlas Liions maki biyar, inda ta dara Uganda da maki guda.

Zimbabwe ma ta samu nasara ne da maki biyar bayan da ta doke Burkina Faso 1-0.

A wasa na gaba, Zimbabwe za ta kara da Mali.