Blackpool ta kori kocinta Paul Ince

Paul Ince Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin yana fama da koma baya a harkar horas wa

Blackpool ta sallami kocinta, Paul Ince, kasa da shekara guda bayan ya zama kocin kungiyar da take buga Championship.

Ince, mai shekaru 46, ya karbi ragamar horas da kungiyar a watan Fabrairun 2013, bayan tsohon kocinta, Michael Appleton, ya koma Blackburn.

Blackpool tana matsayi na daya a teburi a farkon fara kakar wasan bana, bayan da ta lashe wasanni biyar daga cikin wasanni shida data buga, amma yanzu rabonta da lashe wasa tun watan watan Nuwamban bara.

An dakatar da kocin wasanni biyar a watan Oktoba, ya kuma samu nasara a wasnni 12 daga cikin wasanni 42 da suka kafsa.

Wasan karshe da aka doke kungiyar da ci 2-0 da klub din da yake karshen teburi ya yi ranar Asabar, ya sa mataimakan kocin Alex Rae da Steve Thompson suka bar kungiyar.

Tsohon dan kwallon Manchester United da Inter Milan da Liverpool da Ingila mai wasan tsakiya ya horas da Macclesfield Town da MK Dons da Blackburn da Notts County.