Sunderland ta dauki gola Oscar Ustari

Oscar Ustari Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sunderland na kokarin cigaba da zama a Premier

Kungiyar Sunderland ta dauki dan kwallon Argentina Oscar Ustari da zai buga wasanni har karshen kakar wasan bana.

Dan wasan mai shekaru 27, kwangilarsa ta kare da Almeria ta Spain ranar Talata, ya kuma bugawa Argentina wasanni biyu.

Ya kuma zamo dan wasa na uku da kungiyar ta dauko da suka hada da Marcos Alonso da Santiago Vergini.

Sunderland za ta kara da Manchester United, karawa ta biyu a gasar League Cup wasan daf da na karshe ranar Laraba, inda ake sa ran Ustari zai zauna a benci a wasan.

Vito Mannone ne golan kungiyar a yanzu, ya kuma kama wasannin Premier 13, tun lokacin da Kieran Westwood, golan da yake kamawa kungiyar kwallo ya ji rauni a kafada.