Anelka ya musanta "kyamar Yahudu"

Image caption Anelka ya ce ya yi nunin ne don goyon bayan mai ban dariyar Faransa, Dieudonne M'bala M'bala.

Nicolas Anelka ya yi kokarin kare nunin da ya yi da hannunsa, inda ya sa wani bidiyo na fitaccen malamin Yahudawa da ya ce wannan alamar ba ta nufin kyamar Yahudu idan aka yi amfani da ita a filin kwallo.

Anelka mai shekaru 34 na fuskantar dakatarwa daga wasanni biyar, idan hukumar FA ta same shi da laifin yin nunin "cin mutunci" a wasansu da West Ham ranar 28 ga Disamba.

Dan wasan na West Brom ya sa bidiyon a shafinsa na Twitter ne sannan ya ce: "Babu abinda zan kara".

Mutumin dake cikin bidiyon dai shi ne Roger Cukierman, shugaban kungiyar Yahudawan Faransa kuma mataimakin shugaban kungiyar Yahudawan duniya.

Anelka dai na da wa'adin karfe shida na yammacin Alhamis ya mai da martani ga tuhumar FA mai shafuka 34.