United ta taya Mata fan miliyan 35

Juan Mata Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mata baya buga wasa a kai a kai a kakar bana

Manchester United ta taya dan kwallon Chelsea mai wasan tsakiya, Juan Mata, kan fan miliyan 35.

An sha yin rade radin cewa Mata, mai shekaru 25, zai bar Stamford Bridge saboda ba ya buga wasanni a kai a kai a karkashin koci Jose Mourinho.

United ta karyata taya dan wasan, amma tun a farko tayin an yi shi ne tsakanin wasu kamfanunnuka da suke wakiltar Zakarar kofin na Premier.

Mata bai buga atisaye da Chelsea a ranar Laraba ba.

Ranar Talata Chelsea ta jaddada cewa Mata, wanda kungiyar ta zaba dan kwallon da ya fi fice a shekaru biyu a jere, ba na sayarwa ba ne.

Sai dai an sauya dan wasan a karawa tara da ya bugawa kungiyar wasa a kofin Premier a kakar bana, dalilan da ya kawo rade radin dan wasan zai bar kungiyar a Janairu.