City ta kai wasan karshe na League

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Manchester City ta kafa tarihin kwallaye a kofin League

Manchester City ta isa wasan karshe na gasar League Cup a karo na farko cikin shekaru 38 bayan da ta lallasa West Ham 9-0 a wasannin kusa da na karshe.

Alvaro Negredo da Sergio Aguero ne suka zura kwallaye a karonsu na biyu a Upton Park bayan da City ta ragargaji West Ham 6-0.

City za ta kara da Manchester United ne ko Sunderland a filin Wembley ranar 2 ga Maris.

United za ta karbi bakuncin Sunderland ne a wasansu na biyu a matakin kusa da na karshe bayan da Sunderland ta yi nasara a kanta da 2-1 a karawarsu ta farko.

Kocin City Manuel Pellegrini dai ya ce burinsa a bana shi ne ya daga kofuna hudu da suka hada da Premier, Kalubale, League da Zakarun Turai a shekararsa ta farko a Etihad.