Nadal ya doke Dimitrov.

Rafeal Nadal
Image caption Dan wasan zai kara da Federer a wasa mai zafi

Rafeal Nadal ya kaucewa zamowa daya daga cikin 'yan wasan da a kayi waje dasu a gasar kwallon Tenis da Australiya ke karbar bakunci bayan da ya doke Grigor Dimitrov.

Nadal, wanda yake na daya a jerin wadanda su ka fi iya kwallon Tenis a duniya ya doke Dimitrov ne dai da ci 3-6 7-6 (7-3) 7-6 (9-7) 6-2.

Nadal ya ce "Na yi sa a matuka da ya kuskure kwallon dana buga masa cikin sauki har karo biyu."

Dan wasan zai kara da zakaran kofin karo hudu Roger Federer a wasan kusa da na karshe, bayan da Federer ya yi waje da Andy Murray.