Mido ya zama kocin Zamalek

Hassan Mido
Image caption Mido ya buga wasa a kungiyoyin Turai da dama

Tsohon dan kwallon Tottenham da Masar Ahmed 'Mido' Hossam ya zama kocin kungiyar Zamalek ta Alkahira.

Dan shekaru 30, shi ne koci mafi karancin shekaru a tarihin kwallon Masar inda ya maye gurbin Helmi Toulan.

Mido ya soma taka leda ne a Zamalek, ya yi fatali da ake yamadidin ce wa yi karami ya karbi ragamar horas wa.

Mido ya shaidawa gidan talabishin a Masar ce wa "dukkan wadanda suke ganin nayi kankanta ba wani damuwa, amma a Nahiyar Turai ba matsala ba ce, kuma a shirye nake da tunkarar kalubalen da ke gabana."

"Musamman da na dunga daukar shugabancin 'yan wasa a fili."

Zamalek tana daga cikin kungiyoyin da suka yi fice a Afirka, sun dauki kofin zakarun Afirka sau biyar da kuma lashe kofin Masar karo 11.

Duk da lashe kofin Masar a bara, kungiyar ta kasa hada kafada da abokiyar hamayyarta kuma zakarar kofin Afirka karo bakwai Al Ahly a shekarun baya.

Bayan karawa a wasanni 4 da aka shiga sabuwar kakar wasa Zamalek tana matsayi na hudu da tazarar maki shida tsakaninta da Ismaili da kuma tazarar wasa daya.

Mido, ya yi ritaya daga kwallo a bara, bayan da ya bugawa Barnsley dake gasar Championship wasanni.

Tsohon dan kwallon Masar ya dauki kofin Afirka da Masar a shekarar 2006 duk da sun samu matsala da tsohon koci Hassan Shehata.

Ya bugawa Zamalek wasanni kafin ya koma Ajax da Marseille da Roma da Tottenham da West Ham.