CHAN: Zakara zai karbi $750,000

chan 2014
Image caption kasashen za su rage matsalar kudi da su ke fama

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta bayyana cewar zakaran bana a gasar kofin Afirka ta 'yan wasan dake taka leda a gida zai karbi $ 750,000.

Caf ta sanar da yawan kudin da za a lashe ne a daidai lokacin da kasashen za su fafata a wasan daf da na kusa da karshe a karshen makon nan.

Lashe kudin zai karkafawa kasashe takwas da suka rage a gasar da ake karawa a Afirka ta kudu, musamman ma Najeriya da take da matsalolin kudi.

Jimillar sama da Dala miliyon uku za a rabawa kasashe 16 da suka shiga gasar a bana.

Najeriya ta yi kaurin suna akan matsalar rashin kudi, 'yan wasanta sun sha yin barazanar kaurace wa wasa idan kasar ta rage ladan wasan kwallo.

Kuma Koci Stephen Keshi ya share watanni bakwai ba tare da an biya shi albashi ba.

Nigeria za ta kara da Morocco a Cape Town ranar Asabar a wasan daf da na kusa da karshe, sai wasa tsakanin Mali da Zimbabwe.

Ranar Lahadi Gabon ce za ta kara da Libya a Polokwane bayan an tashi wasa tsakanin Ghana da Jamhuriyar Congo a Mangaung.