Chelsea ta dauki Salah daga Basel

Mohamed Salah Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Liverpool ta yi kokarin daukar dan wasa a Janairu

Chelsea ta cimma yarjejeniyar daukar dan kwallon Alkahira Mohamed Salah daga kungiyar Basel ta Switzerland.

Salah, mai shekaru 21, har yanzu bai je an duba lafiyarsa ba ballantana ya amincewa da kwangilar, amma ana sa ran zai ziyarci Stamford Bridge da kuma amincewa da kwantaragin da za ta kai fan miliyan 11.

Liverpool abokiyar hamayyar Chelsea ta taba tattaunawa da Basel da nufin daukar Salah zuwa kungiyar a watan Janairun bana.

Chelsea ta amince ta sayar wa Manchester United Juan Mata ranar Laraba.