Ba mu cancanci kai wa wasan karshe ba-Moyes

David Moyes Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kungiyar na fama da koma baya a kakar bana

Kocin Manchester United David Moyes ya amince cewa kungiyarsa ba ta cancanci kai wa wasan karshe a kofin Capital One Cup ba bayan da Sunderland ta doke ta a Old Trafford.

Sunderland ta samu nasara ne a bugun fenareti da ci 2-1, za kuma ta kara ne da Manchester City a Wembly ranar 2 ga watan Maris.

Moyes ya ce, "ban ji dadi ba matuka, ba mu taka kwallon da ta dace a karawar ba."

United ta yi rashin nasara a karawar farko a Stadium of Light da ci 2-1, a wasa na biyu Jonny Evans ya zura kwallo a minti na takwas kafin aje hutun rabin lokaci.