Chelsea ta sayar wa United Juan Mata

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Juan Mata ya zura kwallaye a ragar Man United a baya.

Chelsea ta amince da tayin £37miliyan da Manchester United ta yi na sayen dan wasanta na tsakiya dan kasar Spain, Juan Mata.

Za a yi wa dan wasan mai shekaru 25 gwajin lafiya ranar Alhamis kafin komawarsa kungiyar mai rike da kambun rukunin Premier.

Ana sa ran Mata zai kulla yarjejeniyar shekaru hudu da rabi ne a Old Trafford.

Dan kwallon da ya buga wa Spain wasa sau 32 ya yi sallama da 'yan wasa da jami'an Chelsea a filin horonsu na Cobham ranar Laraba.

Karin bayani