Southampton ta dakatar da Osvaldo

Dani Osvaldo Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ya taba naushin dan kungiyarsa a Roma

Southampton ta dakatar da dan wasanta mai zura kwallo a raga Dani Osvaldo na makwanni biyu, bayan da ya samu rashin jituwa tsakaninsa da abokin kwallonsa Staplewood a filin atisaye.

Dan kwallon Italiya mai shekaru 28, ya zamo dan wasan kungiyar mafi tsada da ta sayo daga AS Roma a bara kan kudi fan miliyan 15.

Kungiyar bata sanar da takaimaiman abinda ya faru tsakanin 'yan wasan ba.

Sai dai a sanarwar da Saints ta bayar ta ce "Kungiyar ta dauki matakin da ya dace bisa karya ka'ida da dan wasan ya yi".

A farkon watannan, hukumar kwallon Ingila ta dakatar da Osvaldo buga wasanni uku da tarar fan 40,000 bayan da ya shiga kace-nace a karawar da su ka yi da Newcastle a wasan da suka tashi babu ci a Disamba.

Tsohon dan kwallon Espanyol da aka haifa a Argentina ya zura kwallaye uku a wasanni 13 da ya buga Premier a kakar wasan bana.