Li Na da Cibulkova sun kai wasan karshe

Li Na Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karo na uku kenan tana kaiwa wasan karshe

Li Na da Cibulkova za su kara a wasan karshe a kwallon Tennis da Australiya ke karbar bakunci bayan da dukkansu su ka samu nasara a wasan kusa dana karshe da su ka buga.

Li Na ta doke matashiyar 'yar wasa Eugenie Bouchard, da ci 6-2 da 6-4 ta kuma samu damar zuwa wasan karshe karo na uku a Melbourn.

Cibulkova ta kai wasan karshe a karon farko, bayan data yi waje da Agnieszka Radwanska wacce take matsayi ta biyar a jerin 'yan kwallon Tennis a duniya.

Tun a wasan farko Cibulkova 'yar wasan Slovakia ta fara lashe wasan farko kuma ta dore da da haka har ta kammala lashe sauran wasannin.