Capello ya sabunta kwangilarsa da Rasha

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fabio Capello

Kocin Rasha Fabio Capello ya sabunta kwangilarsa don ci gaba da jan ragamar tawagar kasar har zuwa gasar cin kofin duniya na shekara ta 2018.

Dan shekaru 67, ya soma jagorancin tawagar ne a shekara ta 2012 inda ya maye gurbin Dick Advocaat.

Shi ne ya jagoranci Rasha ta samu gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a buga a Brazil.

Kasar Rasha ce za ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018 kuma Capello ya ce " Muna da shiri na musamman ta yadda 'yan Rasha za su yi murna".

Kafin ya ja ragamar tawagar 'yan kwallon Ingila, ya lashe kofuna tara a Italiya da Spain tare da AC Milan da Real Madrid da kuma AS Roma.

Karin bayani