Al Rayyan ta dauki Ayegbeni

Yakubu Ayegbeni
Image caption Dan wasan ya buga wasa a kungiyoyi da dama

Kungiyar Al Rayyan ta dauki dan kwallon Najeriya Yakubu Ayegbeni daga Guangzhou R&F ta China, sai dai ba a bayyana kudin data dauki dan kwallon ba.

Dan wasan mai shekaru 31 ya rattaba kwangilar shekara daya da rabi da kungiyar da ke Qatar.

Yakubu ya koma Guangzhou R&F ne a watan Yuni a shekarar 2012, bayan da ya bugawa Portsmouth da Middlesbrough da Everton da Leicester City da Blackburn Rovers wasanni.

Dan wasan ya zura kwallaye 25 a wasanni 45 da ya bugawa Guangzhou R&F ta China.

Ya fara kwallo a Julius Berger ta Lagos, daga baya ya koma Israel da kungiyar Maccabi Haifa wasa.