Chelsea ta kammala cinikin Salah

Mohamed Salah Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasan ya zabi Chelsea ne dai a kan Liverpool

Chelsea ta kammala cinikin dan kwallon Masar mai buga wasan tsakiya Mohamed Salah daga Basel kan kudi kimanin £11miliyan.

Blues ta bada sanarwar kammala cinikin dan wasan ne dai daf da lokacin da za ta kara da Stoke City ranar Lahadi a kofin FA.

Salah ya buga wa Basle wasanni 47 ne dai tun lokacin da ya koma kungiyar a Yunin shekarar 2012 ya kuma zura kwallaye tara a raga.

Shi ne kuma dan kwallo na uku da Mourinho ya kawo Chelsea a Janairu na, bayan daukar Nemanja Matic da Bertrand Traore.

Chelsea ta kammala cinikin dan wasan ne bayan data sayar da Juan Mata ga Manchester United kan kudi £37 miliyan ranar Asabar.

Abokiyar hamayyar Chelsea wato Liverpool ta so daukar dan kwallon, amma ya gwammace ya zabi Chelsea a kan Liverpool.