Wawrinka ya lallasa Nadal a Tennis

Stanislas Wawrinka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Karo na farko da ya lashe Grand Slam

Stanislas Wawrinka ya zama zakaran gasar kwallon tennis ta Autralia Open bayan da ya lallasa dan wasan tennis na daya a duniya Rafeal Nadal.

Dan kasar Switzerland ya lashe wasanne da ci 6-3 6-2 3-6 6-3, bayan da Nadal ya karasa wasan da rada-din ciwon baya.

Wawrinka mai shekaru 28 ya zama dan wasan Swiss na biyu da ya lashe Grand Slam bayan Roger Fereder zakarar karo 17.

Haka kuma ya zama na farko da ya dauki Grand Slam, wanda baya cikin zakaru hudu da suka hada da Nadal da Federer da Novak Djokovic da Andy Murray tun lokacin da Juan Martin Del Potro ya lashe US Open a shekarar 2009.