West Ham ta dauki Borriello da Nocerino

Marco Borriello Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zai yi wasa a West Ham zuwa karshen kakar bana

West Ham ta dauki dan kwallon Roma Marco Borriello da dan wasan AC Milan Antonio Nocerino a aro zuwa karshen kakar bana.

'Yan kwallon biyu dake bugawa Italiya wasa, Borriello mai zura kwallo a raga ya buga mata wasanni bakwai, Shi kuwa Nocerino mai wasan tsakiya ya taka mata wasanni 15.

Borriello, mai shekaru 31 ya bugawa Roma wasanni 11 a kakar bana ya kuma zura kwallo daya kacal.

Nocerino, mai shekaru 28 ya bugawa Milan wasanni 16 har da gasar kofin zakarun Turai.

Kocin West Ham Sam Allardyce yana ta kokarin karfafa kungiyar kada ta fado daga gasar Premier, kuma ba a sayar masa da dan kwallon Leeds United mai zura kwallo a raga Ross McCormack da ya taya ranar Juma'a.