CAF 2015: An fitar da jadawali

Afcon Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashe 30 ne za su fara wasannin share fage

Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka, wato Caf, ta fitar da jadawalin yadda kasashe za su fafata domin samun gurbi a Gasar cin Kofin Afirka ta 2015 wadda Morocco za ta karbi bakunci.

Za a fara wasannin share fage ne da kasashe 30 domin za kulo wadanda za su shiga wasannin rukuni.

An baiwa kasashe 21 daga cikin 51 tikitin buga wasannin rukunnai kai tsaye.

Za a raba kasashe 28 zuwa rukunnai bakwai, a kowanne rukuni za a dauki ta kasa ta farko da ta biyu da kuma kasashe da za su kare a matsayi na uku da kyakkyawan sakamako da za su hadu da mai masaukin baki Morocco.

Kasashen da suka sami tikitin buga wasan rukunnai: Nigeria, Ghana, Ivory Coast, Zambia, Burkina Faso, Mali, Tunisia, Algeria, Angola, Cape Verde, Togo, Egypt, South Africa, Cameroon, DR Congo, Ethiopia, Gabon, Niger, Guinea, Senegal, Sudan.

Za a fara wasannin share fage ne tsakanin 27 Afirilu a Cairo, Masar ba Morocco da aka sanar a baya ba.

Kwamitin Caf ya kuma sanar cewa kasashe shida na zawarcin daukar nauyin gasa ta shekarar 2019, da kuma kasashe uku dake zawarcin gasa ta 2021.

Kasashen da ke neman bakuncin gasa ta 2019 sun hada da Algeria da Cameroon da Ivory Coast da Guinea da DR Congo da kuma Zambia.

Algeria da Ivory Coast da kuma Guinea sune suke neman daukar bakuncin gasa ta 2021.

Libya ce ya kamata ta karbi bakuncin gasar 2017 kasancewa sunyi musaya da Afirka ta kudu wacce ta gabatar da gasa ta 2013.

Kwamitin Caf zai zabi kasashen da za su dauki bakuncin gasar 2019 da 2021 a taron da za su gabatar a watan Satumbar 2014.