CHAN: Ghana za ta kara da Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Magoya bayan Ghana na sa ran doke Nigeria

Ghana za ta kara da Nigeria a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin kasashen Afrika ta 'yan wasa masu buga kwallo a gida bayan da ta yi nasarar 1-0 kan DR Congo.

Kungiyar Black Stars din ta samu nasarar ne sakamakon fenaritin da Kwabena Adusei ya buga a minti na 69 da take wasa a filin Free State da ke garin Bloemfontein.

A daya wasan daf da na kusa da na karshen da aka buga ranar Lahadi, Libya ta doke Gabon 4-2 da fenariti bayaan da aka kammala wasa da karin lokaci 1-1.

Yanzu haka dai Libya za ta kara da Zimbabwe, wacce ta casa Mali ranar Asabar.

Ranar Laraba 29 ga Janairu za a gudanar da wasannin kusa da na karshen.