Na kagu na buga kwallo da Rooney- Mata

Juan Mata
Image caption Mata ya kagu ya fara bugawa United wasanni

Dan kwallon da Manchester United ta sayo mafi tsada Juan Mata ya ce ya kagu ya buga wasa tare da Wayne Rooney.

Ana rade-radin cewa zuwan Mata Old Trafford daga Chelsea kan kudi £37.1Miliyan, zai kai ga Rooney ya koma Chelsea a karshen kakar bana.

Sai dai kuma Rooney, mai shekaru 28 yana tattaunawa da United domin tsawaita kwangilarsa.

Mata ya ce "Ni kam shi ne dan kwallon da yafi fice a tarihin 'yan wasan Ingila. Dan wasa ne da ba kamarsa."

Ana tunanin Mata ya rattaba kwangilar da zai bugawa United wasanni har zuwa karshen kakar 2018 ana kuma hangen wasansa da Rooney zai kayatar matuka.