Tsauwala farashin wasan Arsenal da Liverpool

Liverpool Supportes Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal ta amince da rage kudin tikiti a kofin FA

Tikitin karawa tsakani Arsenal da Liverpool a kofin FA a Emirates zai zama jerin mataki na biyu, hakan na nufin kudin kallon wasan bazai yi tsadar da 'yan kallo ba za su kasa biya ba.

Magoya bayan Liverpool ne dai tun farko suka yi korafi a rubuce zuwa kungiyoyin biyu cewar kudin kallon da kungiyoyin za suyi a wasan zagaye na biyar a kofin FA ya yi tsada.

Magoya bayan sun bada misalin lokacin da tikiti ya yi tashin gwauron zabi daga £62 zuwa £93 a lokacin da suka ziyarci Emirates a Nuwamba aka kuma doke Liverpool da ci 2-0.

A yanzu magoya bayan Liverpool 9,000 ana sa ran za su biya abinda ya kama daga £35.50 zuwa £54 a filin Emirates.

Arsenal ta kuma dage da cewar daukar matakin da tayi, ya biyo bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki na kungiyar ne.