Cabaye zai koma PSG daga Newcastle

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yohan Cabaye ya ci kwallaye 17 a wasanni 79.

Newcastle da Paris St-Germain sun amince da farashin £20 miliyan na cikin dan wasan tsakiya, bafaranshe Yohan Cabaye.

Ranar Lahadi Newcastle ta ki amincewa da tayin £14 miliyan da PSG ta yi wa dan wasan mai shekaru 28 wanda ya fara wasa a kungiyar cikin 2011.

Amma yanzu sun amince da farashin £19 miliyan zuwa £20 miliyan.

Cabaye, wanda ya ci kwallaye 17 a wasanni 79 zai isa Paris ranar Talata domin gwajin lafiyarsa kuma ba zai buga wasan Newcastle da Norwich na rukunin Premier ba.