An bai wa Salah kyauta a Switzerland

Mohamed Salah Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan da ya yi fice a Switzerland a bara

Sabon dan kwallon da Chelsea ta sayo dan kasar Masar, Mohamed Salah shi ne ya lashe kyautar dan wasan da yafi fice a Switzerland a bara.

Dan wasan mai buga tsakiya magoya baya ne su ka zabe shi ya kuma shiga cikin 'yan kwallo 11 da ba kamarsu a taka kwallo a kasar.

Salah bai halarci bikin karabar kyautar ba a ranar Litinin domin ya tsaya kammala yarjejeniyarsa da Chelsea.

Dan shekaru 21, ya kuma lashe kyautar Golden Player ta shekarar 2013 da kungiyar 'yan kwallon Switzerland ta zabe shi da yafi taka rawar gani a Disambar bara.

Shugaban kungiyar Basel Bernhard Heusler, ne ya karbi kyautar a madadin dan wasan ya kuma yi alkawarin zai ba Mohamed kyautar hannu da hannu.

A bara, Salah ya taimaka wa Basel lashe gasar kofin Swiss da kuma karewa a matsayi na biyu a gasar Swiss Cup.

Kyautar da ya lashe, alkalai ne daga bangaren Kociyoyi da Kaftin kaftin da 'yan jaridu suke haduwa su fitar da zakara.