Stoke ta kammala sayen Odemwingie

Odemwingie Kenwyne Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Musayar 'yan wasa tsakanin Stoke da Cardiff kenan

Stoke City ta kammala sayen Peter Odemwingie daga Cardiff City a yarjejeniyar musayar 'yan wasa a inda Kenwyne Jones zai koma Cardiff City.

Dan wasan Najeriya ya rattaba hannu a yarjejeniyar watanni 18 da Stoke, kuma shi ne dan kwallon na uku da kungiyar ta dauko a Janairun nan, bayan da ta sayi Stephen Ireland da yake aro daga Aston Villa ya zama dan kwallonta dungurungum da kuma John Gudietti daga Manchester City.

Ranar Talata aka kammala yarjejeniya da Odemwingie, kuma koci Mark Hughes yana fatan saka shi a karawar da kungiyar za ta yi da Sunderland a filin Stadium of Light a ranar Laraba.

Odemwingie ya koma Cardiff ne daga West Bromwich Albion a Satumbar bara, ya zura kwallaye biyu a wasanni 17 da ya bugawa kungiyar.

Dan wasan da ya fara kwallo a Najeriya ya yi wasa a Belgium da Faransa da Rasha, kuma ya yi fice ne a West Bromwich a inda ya buga wasanni 87 ya kuma zura kwallaye 30.

Odemwingie, mai shekaru 32, ya buga wa Super Eagles wasanni 55 ya kuma zura kwallaye tara