PSG ta kammala cinikin Cabaye

Yohan Cabaye Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Cabaye zai koma wasa a PSG ta Faransa

Kungiyar Paris St-Germain ta Faransa ta kammala cinikin dan wasan Newcastle mai buga tsakiya, Yohan Cabaye, kan kudi £19 miliyon.

Dan kwallon mai shekaru 28, ya amince da kwantiragin shekaru uku da rabi, bayan da likitocin kungiyar suka duba lafiyarsa ranar Laraba.

PSG wacce take ja gaba a teburi a gasar Faransa, ta fara taya Cabaye kan £14miliyan ranar Lahadi, daga karshe suka sake tayin da bai kai £20 miliyan.

Dan kwallon Faransa ya koma Newcastle ne dai a £4.3 miliyan a watan Yunin 2011, ya kuma zura kwallaye 17 a wasanni 79 da ya buga.

PSG ta bai wa AS Monaco tazarar maki uku a teburi, kuma za ta kara da Bayer Leverkusen a gasar kofin zakarun Turai na kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.