Newcastle ta taya Clement Grenier

Clement Grenier
Image caption Newcastle na kokarin kawo sabbin 'yan wasa kungiyar

Newcastle ta taya dan kwallon Lyon, Clement Grenier domin maye gurbin Yohan Cabaye kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasan kwallon kafa.

Dan kwallon Faransan ya zura kwallaye 12 a wasanni 89 da ya bugawa Lyon wasanni.

Ana sa ran Cabaye zai kammala koma wa Paris St-Germain ranar Laraba kan kudi £20 miliyan, kuma likitocin kungiyar Newcastle sun duba lafiyar dan wasa Borussia Monchengladbach Luuk de Jong da zai buga mata wasa a aro.

Grenier yana daga cikin jerin 'yan wasan da Newcastle take zawarci amma koci Remi Garde baya son ya rabu da dan wasan a yanzu.

Kocin Newcastle Alan Pardew ya roki mamallakin kungiyar Mike Ashley da daraktan wasanni Joe Kinnear da su ware wani kaso na kudin sayar da Cabaye domin sayo wasu 'yan wasan.

Newcastle za ta kara da Sunderland a wasan hamayya ranar Asabar.