Mourinho ya soki salon kwallon West Ham

Jose Mourinho
Image caption Kwallon Mutanen da West Ham suke buga wa.

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya soki salon kwallon da West Ham take bugawa da irin ta karni na 19 ce, bayan da suka tashi wasa babu ci a kofin Premier da suka kara ranar Laraba.

Chelsea ta kai hare-hare 39, Westham sau daya kacal ta kai hari a karawar da ta tsare gidanta har aka tashi.

Mourinho ya ce "ba irin wannan wasan ya kamata ace suna buga waba, domin salon wasa ne na mutanen da."

Duk da kokarin da Chelsea ta yi na zura kwallo, kwallaye tara ne suka nufi raga kai tsaye, golan Hammers Adrian ya hana kwallo ta shiga raga har karo uku da John Terry da Samuel Eto'o da Frank Lampard suka buga masa.

Dan wasan Brazil Oscar da kuma Demba Ba da ya shiga wasa canji sun buga kwallo ta doki turke.