Ghana ta fitar da Nigeria a CHAN 2014

Image caption Ghana ko Libya za ta daga kofin CHAN a bana.

Ghana ta doke Nigeria yayin da Libya ta doke Zimbabwe duk a bugun fenariti inda su ka samu damar buga wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Afrika ta 'yan kwallo masu buga wasa a gida, CHAN 2014.

Ghana ta yi nasarar 4-1 a bugun fenariti, bayan da ta rike Nigeria aka tashi wasa da karin lokaci canjaras duk da jan katin da aka ba Kwabena Adusei a minti na 64 da take kwallo.

Libya kuma ta doke Zimbabwe 5-4 ne bayan da suka kammala wasa babu kwallo ko daya.

Libya da Ghana za su buga wasan karshe ranar Asabar a Cape Town da karfe 1800 GMT.