Emordi ya zama kocin Kano Pillars

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Web Page
Image caption Zakarar kofin Premier a Nageriya a kakar bara

Zakarar kofin Premier a Najeriya Kano Pillars, ta dauki Okey Emordi a matsayin sabon kocinta.

Shugaban kungiyar Abba Yola wanda ya sanarda haka ya ce Emordi zai jagoranci kungiyar a tsawon kakar wasa daya, bayan da ya karbi aiki daga hannun Baba Ganaru wanda ya koma kocin Nasarawa United.

Tsohon kocin Enugu Rangers ya jagoranci Enyimba da ta lashe kofin zakarun Afirka a shekara ta 2004, ya nemi aikin ne tare da tsohon kocin Pillars Khadiri Ikhana.

Kano Pillars za ta fara ziyartar As Vitalo ta Jamhuriyar Congo a kofin zakarun Afirka a Fabrairu.