Man City ta karbi ragamar Premier

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Raunin Sergio Aguero ne kawai cikas din da City ta samu a wasan.

Manchester City ta karbe ragamar rukunin Premier inda ta dara Arsenal da maki guda, bayan da ta lallasa Tottenham 5-1 a filinta na White Hart Lane.

Sergio Aguero ne ya fara zura kwallo inda ya ci kwallonsa ta takwas cikin wasanni takwas a jere.

Yaya Toure ya kara ta biyu da bugun fenaritin da ya jawo kace-nace bayan da aka bai wa dan bayan Tottenham, Danny Rose jan kati bisa laifin take Edin Dzeko.

Dzeko ne ya kara ta uku, kuma duk da Etienne Capoue ya zare wa Tottenham daya, sai da Stevan Jovetic ya samu zura kwallonsa ta farko a Premier tun bayan sayo shi kan £22 miliyan daga Fiorentina.

Kafin tashi daga wasa kuma, kyaftin din Manchester Vincent Kompany ya zura kwallon karshe.

Cikas daya da Man City ta samu a wasan shi ne raunin da Sergio Aguero ya yi, abinda zai iya sa ya kasa buga wasan makon gobe da kungiyar za ta hadu da Chelsea.