Newcastle ta daukaka kara kan jan katin Remy

Loic Remy Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Loic Remy ba zai buga karawa a wasanni uku ba

Newcastle United ta dauka ka kara a kan jan katin da aka baiwa Loic Remy da ba zai buga wasanni uku nan take ba, a karawar da su ka yi da Norwich suka ta shi wasa ba bu ci.

Remy, mai shekaru 27, an bashi jan kati tare da dan wasan Norwich Bradley Johnson bayan da 'yan wasan suka yi rigima afili.

Kungiyar ta ce ta mika korafi ga hukumar FA saboda korar da aka yi wa dan wasanta bai dace ba.

Idan FA ba ta amince da dauka ka karar ba, Remy ba zai buga karawar da kungiyar za ta yi ba da Sunderland ranar Asabar da kuma wasan Chelsea da Tottenham.

Magpies za ta ziyarci filin Stamford Bridge ranar 8 ga watan Fabrairu, sannan ta karbi bakuncin Tottenham ranar 12 ga watan Fabrairu.

Itama Norwich ta sanar da cewa za ta daukaka karar jan katin da aka baiwa dan wasanta Johnson a minti na 81 ana wasa.