Yobo ya koma Norwich

Joseff Yobo Hakkin mallakar hoto empics
Image caption Dan kwallon Najeriya tsohon dan wasan Everton

Norwich City ta dauki dan wasan Fenerbahce kumu tsohon dan wasan Everton mai tsaron baya Joseph Yobo a aro da zai buga mata kwallo zuwa karshen kakar bana.

Dan kwallon Najeriya mai shekaru 33 ya kwashe shekaru 10 a Toffees daga shekarar 2002 zuwa 2012, ya buga mata wasanni 258.

Yobo tsohon dan kwallon Marseille ya bugawa Fenerbahce wasanni biyu kacal a kakar bana, har da gasar kofin zakarun Turai da Arsenal ta doke su da ci 3-0 a watan Agusta.

An zurawa Norwich kwallaye 35 a raga a wasannin kofin Premier 23 data kara a bana.