Aguero zai jinyar wata daya

Image caption Sergio Aguero

Dan kwallon Manchester City Sergio Aguero zai yi jinya wata guda.

Dan Argentinan mai shekaru 25, ya ci kwallo daya a wasan da City ta doke Tottenham daci biyar da daya.

Kenan ba zai buga wasanninsu da Chelsea, Norwich, Sunderland da kuma Stoke.

Aguero yana haskakawa a kakar wasa ta bana inda ya ci kwallaye da dama.

A yanzu haka City ce kan gaba a saman teburin gasar inda take gaban Arsenal.

Karin bayani