Man City za ta dau 'yan wasan Porto

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An yi wa Mangala farashin £35 miliyan.

Manchester City na neman dauko 'yan wasan Porto guda biyu; Eliaquim Mangala da Fernando.

Kocin City Manuel Pellegrini dai bai ba da cikakken bayani game da sababbin 'yan wasan da zai dauka ba.

Sai dai mai yiwu wa ne 'yan wasan biyu su koma City kafin rufe kasuwar 'yan wasa ranar Juma'a.

An yi wa dan bayan Faransa, Mangala mai shekaru 22 farashin £35 miliyan kuma ya na cikin 'yan wasan da ake ji da su a Turai, yayin da Fernando mai shekaru 26 zai kara wa tsakiyar City karfi.

Sai dai Manchester United da Paris St-Germain ma na zawarcin Mangala.

Shi kuma Fernando ya na cikin wadanda Everton da AC Milan ke nema.