Arsenal ta doke Palace da ci 2-0

Alex Oxlade-Chamberlain
Image caption Karon farko da Chamberlain ya zura kwallo a bana

Arsenal ta dare teburin Premier bayan data doke Crystal Palace da ci 2-0 a filin Emirate wasan mako na 23.

Alex Oxlade-Chamberlain shi ne ya fara zura kwallon farko, kuma kwallonsa na farko a kakar bana, bayan da ya buga kwallo ta wuce golan Palace Julian Speroni a lokacin da Santi Cazorla ya bashi dama.

Palace ta kusa farke wasa a lokacin da Cameron Jerome ya kai hari da kansa, sai dai golan Arsenal ya hana kwallo shiga raga.

Oxlade-Chamberlain shi ne dai ya kara kwallo ta biyu a raga bayan da suka yi bani in baka da shi da Olivier Giroud.

Arsenal tana matsayi na daya a teburi da maki 55, ranar Litinin za a karasa wasan mako na 23 tsakanin Manchester City da Chelsea a Ettihad.