CHAN: Keshi ya yaba kokarin 'yan wasa

Steven Keshi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Keshi ya ce 'yan wasa sun taka rawar data dace

Kocin Najeriya Stephen Keshi na alfahari da kwazon da 'yan wasa suka nuna a kofin Afirka duk da kasa kaiwa wasan karshe da Ghana ta fidda su a wasan daf da na karshe.

Super Eagles ta doke Zimbabwe da ci daya mai ban haushi a wasan neman gurbi na uku, wanda Christian Chinonso Obiozor ne ya zura kwallo a raga.

Keshi ya ki yarda ya zargi 'yan Najeriya da kasa doke Ghana duk da ta kammala wasanta da 'yan kwallo 10 a fili.

Najeriya bata sa kaimi a karawar da ta yi da Ghana ba, har ta kai bugun penariti aka kuma fiddda ita a wasan hamayya da suka kara.

Keshi ya ce" Na yi murna da yadda 'yan wasan suka taka kwallo duk da cewa wannan shine karonsu na farko a gasar, ga kuma yadda ake bukatar su kawo sakamako."

"Ina alfahari da su da kuma yadda suka nuna halin da'a a gasar"

Najeriya ta yi rashin manyan 'yan wasa kamar su Sunday Mba da Godfrey Oboabona wadanda suka koma Turai da kwallo, amma Keshi ya ce kwalliya ta biya kudin sabulu, domin 'yan wasa sun kara gogewa.

Bayan kammala gasar Ejike Uzoenyi ya lashe kyautar dan kwallon da yafi fice, haka kuma an zabi Odunlami Kunle da Rabiu Ali cikin fitattun 'yan wasa 11 na gasar.