West Brom da Liverpool sun buga 1-1

Kolo Toure
Image caption Kuskuren da Kolo Toure ya yi aka tashi wasa 1-1

Kuskuren da mai tsaron bayan Liverpool Kolo Toure ya yi, yasa West Brom ta farke kwallon da aka zura mata a gasar kofin Premier wasan mako na 23.

Daniel Sturridge ne ya zura kwallo a ragar West Brom, lokacin da ya samu kwallo daga bugun Luis Suarez.

Albion ta kai harin da kiris kwallon ta shiga raga, lokacin da Gareth McAuley ya buga kwallo da ka amma golan Liverpool Simon Mignolet ya buge kwallo.

West Brom ta farke kwallonta lokacin da Kolo Toure ya bada kwallo bisa kuskure, Victor Anichebe ya zari kwallo ya kuma buga ta shiga raga.

Liverpool tana matsayi na hudu a teburin Premier da maki 47, West Brom kuwa na matsayi na 16 da maki 23.