Munich ta lashe wasanni 44 a Bundesliga

Bayern Munich Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Munich ta bada tazarar maki 13 a gasar Bundesliga

Bayern Munich ta lashe wasanni 44 a jere, bayan da ta casa Eintracht Frankfurt da ci 5-0 ranar Lahadi a kofin Bundesliga.

Mario Gotze shi ne ya zura kwallon farko da ya baiwa Munich damar zura kwallaye 56 a manyan wasannin Turai da kuma zarta tarihin da Arsenal ta kafa na zura kwallaye 55 a shekarar 2001.

Frank Ribery ne ya zura kwallo ta biyu, kafin daga baya Arjen Robben da ya shigo wasa sauyi ya zura kwallo ta uku.

Sauran kwallaye na hudu da na biyar kuwa 'yan wasa Dante da Mario Mandzukic ne suka zura su a raga.

A yanzu lokaci ya rage a bayyana Munich a zakarar kofin Jamus karo na 24, sun bada tazarar maki 13 a teburin Premier.

Bayern Munich zakarar kofin Turai za ta kara da Arsenal a wasan kungiyoyi 16 da suka rage, a kokarin da take na lashe kofin Bundesliga da na zakarun Turai kamar yadda tayi a bara a jere.