CAF: An tsayar da ranar Super Cup

Al Ahly Egypt Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Al Ahly tafi kowacce kungiya yawan lashe Super Cup

Hukumar kwallon kafar Afirka, CAF ta tsayar da ranar Alhamis, 20 ga watan Fabrairu domin karawa a kofin Super Cup a filin wasa na Air Defence da ke Alkahira.

Wasan bugu daya siri kwale, za a kafsa tsakanin Al Ahly ta Masar tauraruwar kofin Champions League da CS Sfaxien ta Tunisia tauraruwar kofin Confederation Cup.

Tun a farko an tsayar da ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu a filin wasa na Cairo International Stadium.

Caf ta ce kwamitin amintattu ne ya yanke shawarar sauya ranar wasan domin bin tsarin hukumar kamar yadda ta tanada.

Wannan shi ne karo na biyu da kungiyoyin za su sake karawa a kofin tun lokacin da suka fafata a shekarar 2009 kuma Al Ahly ta lashe wasan da ci 2-1 a Alkahira.

Al Ahly ce ta fi kowacce kungiya samun gagarumar nasara a kofin Caf Super Cup, ta lashe karo biyar, kuma Sfaxien sau biyu tana daukar matsayi na biyu.