FA ta zargi Norwich da Newcastle

Norwich Newcastle Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Rigingimnu da 'yan wasa suka yi ta yi a wasan da suka kara

Hukumar kwallon Ingila tana tuhumar kungiyoyin kwallon kafa na Norwich da Newcastle bisa kasa tsawatarwa da 'yan wasansu a karawar da suka yi a kofin Premier ranar 28 ga watan Janairu.

A wasan sai baiwa Loic Remy na Newcastle da Bradley Johnson na Norwich jan kati aka yi a filin wasa na Carrow Road, sakamakon rigingimu da fadan da 'yan wasan kungiyoyin suka yi a fili.

FA ta janye jan katin da aka baiwa Johnson bayan da kungiyar ta dauka ka kara, amma ba a janye na Remy ba duk da kungiyarsa ta daukaka kara.

An baiwa kungiyoyin damar kare kansu daga nan zuwa ranar 5 ga watan Fabrairu.