'Na yi dana sanin sayen Kallstrom'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kim Kallstrom na jinyar ciwon baya

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce da yasan cewar dan kwallon Sweden Kim Kallstrom na fama da ciwon baya, to da bai saye shi ba.

Kallstrom mai shekaru 31, ya hade da Gunners a matsayin aro daga Spartak Moscow amma zai yin jinyar makwanni shida.

Wenger ya ce "Na yi dana sannin sayensa".

A yanzu Arsenal ce kan gaba a kan teburin Premier bayan ta doke Crystal Palace daci biyu da nema.

Kallstrom, tsohon dan kwallon Lyon, na cikin rukunin 'yan kwallon Arsenal dake fama da rauni wato kamarsu Aaron Ramsey da kuma Jack Wilshere a yayinda aka dakatar da Mathieu Flamini.

Karin bayani